Wani mutum ya mayar da wani littafin almara game da wata ƙasar kwatance mai taken George Orwell's 1984, zuwa ɗakin karatun Amurka da ke jihar Oregon bayan shekara 65. A wani saƙo da ya rubuta kuma ya cusa a cikin littafin, mutumin mai shekara 86 wanda ya bayyana sunansa da WP kawai ya ce kamata ya yi ya mayar da littafin zuwa ɗakin karatu na Mulnomah da ke Portland saboda fa'idar da yake shi har a zamanin yau. "Bayan sake-karantawa karo da dama, na fahimci cewa, fiye da kowanne lokaci a baya, kamata ya yi a sake buga wannan littafi don samun sa a cikin jama'a," rubutun ya ce. Labarin almarar ya yi nuni ne da taken da ya shafi mulkin kama-karya da kuma tsage gaskiya. "Ya kamata na mayar da wannan littafi ne a 1958, lokacin da nake shirin kammala karatu a [Jami'ar Jiha ta Portland], amma ban samu damar yin hakan ba," ya rubuta a cikin saƙon. "A yi min afuwa kan wannan dogon jinkiri. A shekara 86, ina so a ƙarshe na cire tunanin daga zuciyata,...