Tsohon shugaban EFCC Abdulrashid Bawa na fuskantar tambayoyi da tuhume-tuhume..


 Tsohon shugaban EFCC Abdulrashid Bawa na fuskantar tambayoyi da tuhume-tuhume.. 


Hukumar DSS dai na binciken Bawa, bisa zargin karkatar da dukiyar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kwace daga hannun wadanda ake tuhuma da dai sauransu.


  Wata majiya ta ce: “A shekarar 2019, an kama Bawa, an kuma yi masa tambayoyi kan siyar da manyan motoci kusan 244 da tashar ruwan mu ta kwace.


 Inda ya yi aiki a matsayin shugaban shiyya. Wannan lamari dai na daya daga cikin manya-manyan dalilan da suka sa aka dakatar da shi ana bincike, inda ya sayar da manyan motocin da farashinsu ya kai N20m zuwa N30m inda ya sayar da kowannen su ga wakilansa a kan farashi N100,000 a kowace sashi, wanda ya hana kasar samun kusan N4.8bn 


  Wannan ne ya sa tsohon sakataren EFCC, Ola Olukoyede, ya fuskanci shugaban na EFCC a 2019, saboda an ce ya samu korafe-korafen cewa Bawa na yin kutse a kan kadarorin da ake kwacewa. Amma da aka tambayi Bawa abin da ya faru..akan manyan motocin, ya yi ikirarin cewa yana aiki ne da umarnin tsohon Shugaban, Magu, amma bai taba rubuta haka ba a cikin bayanansa.

 Kuna da masaniya sosai cewa Matawale ya kuma zargi shugaban da neman cin hancin $2m daga gare shi. Wannan ma wani bangare ne na zargin da ake yi.

Comments

Popular posts from this blog