Mutanen da suka mutu bayan hatsarin jirgin ƙasa a Indiya sun kai 30
Hukumomi a jihar Odisha da ke gabashin Indiya sun sanar da mutuwar aƙalla mutum 30 da mutuwar ɗaruruwa sakamakon taho mu gama da wasu jiragen ƙasa guda biyu suka yi.
Kusan motocin daukar marasa lafiya 50 ne aka aika zuwa wurin da lamarin ya faru a Lardin Balasore, a cewar babban sakataren jihar.
Ana kuma fargabar cewa mutane da dama sun rasa ransu.
Firaministan Indiya Narendra Modi ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yake cewa yana cikin matukar damuwa sakamakon hadarin kuma ya na taya wadanda suka rasa 'yanuwansu jimamin rashin.
Taragan jirgi da dama ne suka kauce daga layin dogo.
Ana kuma ci gaba da aikin agaji domin kuɓutar da mutane.
Ana yawan samun haɗarin jirgin ƙasa a India, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
Gwamnatin Senegal ta baza sojoji a fadin Dakar, babban birnin kasar, yayin da mazauna yankin ke zaman dar-dar inda su ke tsammanin ci gaban tashin hankali.
Mutane 9 ne suka rasa ransu a ranar Alhamis sakamakon artabu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga.
Hakan ya biyo bayan yanke hukuncin daurin shekara biyu da aka yi wa dan siyasar nan Ousmane Sonko kan rashin da'a.
Mista Sonko ya ci gaba da cewa tuhumarsa da aka yi na da nasaba da siyasa domin a hana shi tsayawa takara a zaben shugaban kasa na badi.
'Yan sanda sun kewaye gidansa, sannan gwamnati ta rufe wasu shafukan sada zumunta

Comments
Post a Comment