Za muyi amfani da tarkacen rugujewa wajen gyara katangar birnin Kano, inji Abba kabir Yusuf |
Za muyi amfani da tarkacen rugujewa wajen gyara katangar birnin Kano, inji Abba kabir Yusuf |
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta yi amfani da tarkacen wuraren da ake rugujewa domin gyara tsoffin katangar birnin Kano da su lalace,
Abba Kabir Yusuf gwamnan jihar Kano
ya bayyana haka ne bayan ya duba wuraren da ake ruguzawa a cikin birnin Kano. A ranar Juma’ar da ta gabata,
Tare da wasu yan kwamitin kula da rusau ɗin
n kwamitin da gwamnan ya kafa ya fara rusa wasu gine-ginen da ake kyautata zaton an gina a kan filaye mallakar gwamnatin Jihar Kano wanda tsohuwar Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gina,
Wasu daga cikin gine-ginen da aka rusa kawo yanzu sun hada da zagayen da ke kusa da gidan gwamnati, da wani gini mai hawa uku mai shaguna 90 a Nasarawa GRA da shaguna da aka gina a gefen katangar filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata.
Sauran gine-ginen GGSS Dukawuya, Goron Dutse, gine-gine a sansanin Hajjin Kano da Otal din Daula, da dai sauransu.
Yusuf ya ce an ba ‘yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) umarnin kula da wuraren da ake rugujewa daga masu zagon kasa.
“Mun zaga cikin gari domin duba wuraren da aka rushe. Mun yanke shawarar yin amfani da tarkacen wuraren da aka rusa domin gyara katangar birnin Kano don adana tarihi, da kawata jihar da kuma mai da ita wurin sha’awa a matsayin abin tarihi na kasa,” in ji Yusuf.

Comments
Post a Comment